Banbarakwai: Wata matashiya ta auri wani matashi, ta biya danginsa la'adar miliyan N289m
- Wasu sabbin ma'aurata a kasar China sun dauki hankulan ma'abota amfani da kafafen dandalin sada zumunta
- Sabanin abinda aka saba gani a aure, auren matasan ya sha ban-ban, domin kuwa matar ce ta auri mijin
- Amarya, hamshakiyar attajira, ta biya sadakin $104,273 da kuma gida da motar hawa ga sabon angonta
Wani aure tsakanin wasu masoya a kasar Sin (China) ya ja hankulan ma'abota amfani da kafafen sada zumunta saboda sabanin shekaru da arziki dake tsakanin sabbin ma'aurata.
Amarya, hamshakiyar attajira mai shekaru 38, ta auri saurayin masoyinta, matashi mai shekaru 23.
An fara nuna shagalin bikin ne ranar 10 ga watan a Janairu a garin Qionghai dake yankin Hainan a kasar China.
Tunda farko, ance matar ta samu juna biyu da saurayin, shi kuma ya amince ya aureta. Iyayen matashin sun ki amincewa da auren saboda banbancin shekaru 15 dake tsakanin matashin da amaryar.
DUBA WANNAN: Sun yi taron dangi sun kashe babbar soja, sun kone gawar ta
Gabanin daurin auren, amaryar ta biya sadakin matashin $104,273 tare da hada masa da gida da motar hawa da aka yi kiyasin sun kai $789,950. Wannan goma ta arziki ta sanya iyayen matashin amincewa da auren ba tare da kara yin korafin komai ba.
Auren ya jawo cece-kuce a kasar China. Yayin da wasu ke masu fatan alheri suna taya su murna, wasu kuwa cewa suke matashin ya amince da auren matar ne saboda kwadayin abin duniya. Wasu kuwa cewa suke sun ga ikon karfin kudi.
Amarya da ango dai na can suna holewa abinsu cikin farinciki da kwanciyar hankali.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng