PDP ta kyarawa 'yan Najeriya wata sabuwar yaudara da tayi zargin APC na kullawa 'yan Najeriya
- A satin da ya gabata ne jam'iyyar APC ta karbi rahoton kwamitinta a kan yiwa kasa garambawul
- Jam'iyyar hamayya ta PDP ta zargi APC da kokarin yaudarar 'yan Najeriya domin samun kuri'u a zaben 2019
- PDP ta ce jam'iyyar APC ta yaudari 'yan Najeriya a 2015 domin sun gaza cika dukkan alkawuran da suka yiwa jama'a
Jam'iyyar PDP ta yi watsi da rahoton kwamitin jam'iyyar APC a kan yiwa kasa garambawul ya gabatar ga uwar jam'iyyar a satin da ya gabata.
A satin da ya gabata ne kwamitin na jam'iyyar APC karkashin jagorancin gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Elrufa'i, ya mika rahotonsa ga uwar jam'iyyar. Jam'iyyar APC ta karbi rahoton kwamitin da niyyar tabbatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.
Saidai jam'iyyar adawa ta PDP ta ce jam'iyyar APC na kokarin kara yaudarar 'yan Najeriya ne kamar yadda suka yi a shekarar 2015 yayin yakin neman zabe.
DUBA WANNAN: Kungiyar CAN tayi watsi da zargin da kungiyar MURIC ta Musulmi tayi mata
Sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, a wani jawabi da ya yi ga manema labarai ya ce APC na kokarin boye gazawar su ta hanyar fakewa da son yiwa kasa garambawul.
Ologbondiyan ya ce shugabanni da jagororin jam'iyyar APC a baya sunyi watsi da kiraye-kirayen yin garambawul ga Najeriya, a saboda haka yanzu sun bijiro da maganar ne domin samun goyon baya da kuri'u a zaben shekarar 2019.
Jam'iyyar PDP ta ce ya zama tilas ta ankarar da 'yan Najeriya domin kada su fada tarkon yaudarar APC a karo na biyu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng