Babu yadda za a iya kari a cikin kasafin kudin shekara 2018 – Daraektan ofishin hukumar kasafin kudi
- Darekta janar na ofishin hukumar kasafin kudi ya ce matakan da suka dauka yasa baza a iya yin cuwa-cuwa a cikin kasafin kudin shekara 2018 da aka gabatar ba
- Mista Akabueze duk wani kari da aka yi a cikin kasafin kudi 2018 za su sani
Daraekta janar na ofishin hukumar kasafin kudi na Najeriya, Mista Akabueze, ya ce baza a iya yin cuwa-cuwa a kasafin kudin shekara 2018 da gwamnatin tarayya ta gabatar ba.
Akabueze, ya bayyana hakane a lokacin da yake yiwa kungiyoyin kafafen watsa labaru da kugiyoyi masu zaman kan su bayyani akan sauye-sauyen da suka yi a al’amauran da ya shafi kasafin kudi a ranar Laraba a Abuja.

Ya ce bakadalar kasafin kudi ko kara kari a cikin kasafi kudi ba zai yiwu a yanzu ba saboda hukumar ta saka shi a wani shafin yanan gizo mai suna GIFMIS.
KU KARANTA : Obasanjo ya kaddamar da kungiyar gamayyar ‘yan Najeriya da yayi ikrarin zai kafa a Abuja
Akabueze, ya ce duk wani kari da akayi a cikin kasafin kudin 2018 da aka gabatar za su sani.
Yace gwamnatin tarayya a shirye ta ke ta ba da amsa da kan kasafin kudin Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng