Siyasar Kano: Cacar baki tayi tsanani tsakanin Misau da Barau akan Kwankwaso

Siyasar Kano: Cacar baki tayi tsanani tsakanin Misau da Barau akan Kwankwaso

A sakamakon furucin ɗan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Bauchi ta Tsakiya, sanata Hamman Misau dangane da yadda siyasar jihar Kano ta shiga wani fage, wanda a halin yanzu jihar take fuskantar barazanar tsaro, wani abokin aikin sa ya tsawatar da shi akan hakan.

A ranar larabar da ta gabata ne Misau ya bayyana cewa, siyasar jihar Kano ta yi wani sharar fage mai mummunan hatsari da har ya kai matasan na baja kolin muggan makamai domin kare gwarzon su na fagen siyasa.

Sanatan ya ci gaba da cewa, a sakamakon haka ne jam'iyyar APC reshen jihar Kano tayi kutungwilar hana sanata Kwankwaso shiga mahaifarsa a ranar talatar da ta gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, Sanata mai wakilcin mazabar jihar ta Tsakiya bai samu damar ziyartar jihar ba a sakamakon gujewa abin da ka iya afkuwa a cikin ta bayan da fadar shugaban kasa ta shiga cikin lamarin.

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

A yayin haka ne ɗan majalisa mai wakilcin jihar Kano ta Kudu, Sanata Kabiru Gaya, ya bayyana cewa wannan matsalar cikin gida ce, inda ya nemi shugaban majalisar dattawa da cewar wannan ba batun da ya dace ne a tattauna a farfajiyar majalisar ba.

KARANTA KUMA: Hukumar 'yan sanda tayi ram da baƙin haure 84 a birnin tarayya

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, a yayin bayyana na sa ra'ayin dangane da rikicin siyasar jihar, Sanata Jibril Barau ya gargaɗi 'yan majalisar akan kaurace wa batutuwa makamantan haka da cewar matsalar jam'iyya ce da ka iya janyo rabuwar kawuna a majalisar.

Barau ya gargaɗi Misau da cewar ya kasance mai lura da batutuwan da baya da iko a kai kuma ya daina shiga abin da bai shafe shi ba, inda ya kuma tunatar da shi akan warware matsalolin dake tsakanin sa da gwamnan jihar sa.

A yayin tuntubar Sanata Kwankwaso dangane da lamarin ya bayyana cewa, ai ko kadan bai dace ya furta komai ba a halin yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng