Yanzu Yanzu: Matsalar zuciya ya kawo cikas a shari’an Fani-Kayode na zambar kudi
Shari’an tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya samu tsaiko a ranar Laraba, 31 ga watan Janairu bayan lauyansa ya fadawa mai shari’a cewa wanda yake karewa ba zai samu damar halartan kotu ba saboda matsala da ta shafi ciwon zuciya.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Norris Quakers, lauyan Fani-Kayode yace tsohon ministan na fama da ciwon zuciya sannan kuma zai gabatar da rahoton likita daga baya a yau.
Fani-Kayode da Nenadi Usman, wani tsohon karamin ministan kudi na fuskantar tuhuma akan zambar kudi da yawansu ya kai kimanin naira biliyan 4.6.
KU KARANTA KUMA: Manomi ya yabi Buhari bayan ya mallaki naira miliyan daya na kansa daga noman shinkafa
Yusuf Danjuma, wani tsohon shugaban kungiyar kananan hukumomin Najeriya (ALGON) da Jointrust Dimentions Nigeria Limited, ya kasance daga cikin wadanda ake tuhuma a shari’an.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng