Zaben 2019: Atiku ne jirgin ceton talakawa - Inji wata kungiyar Yarbawa
-Atiku ne jirgin ceton talakawa - Inji wata kungiyar Yarbawa
- Shugaban kungiyar matasan mai suna Cif Jackson Lekan Ojo ya bayyana haka
- Cif Ojo ya bayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da majiyar mu a garin Abuja
Shugaban hadakar kungiyar matasan Yarbawan Najeriya mai suna Cif Jackson Lekan Ojo ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya yafi cancanta da ya jagoranci kasar nan ta Najeriya a zabe mai zuwa.
KU KARANTA: Kwamishina ya fadi ana taro a Bayelsa
Cif Ojo ya bayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da majiyar mu a garin Abuja inda kuma ya bayyana cewa tuni ya dauki damarar jan ragamar kungiyar ta sa wajen fara yiwa zabin nasa Kamfe da wuri domin samun nasara.
Legit.ng dai ta samu cewa ya kuma kara da cewa kadan daga cikin dalilan sa na fadar haka shine ganin yadda Atiku din ya samarwa da matasa da dama aiyyukan yi a matsayin sa na dan kasuwa sabanin rasa ayyukan yin da shugaba Buhari ya jawowa kasar.
A wani labarin kuma, Wasu 'yan Najeriya a karkashin inuwar wata jam'iyyar siyasa mai suna New Nigeria Nationalists a turance sun dunguma sun fara tattaki tun daga jihar Legas inda suka kuma nufi garin Abuja domin nuna adawar su ga salon mulkin shugabannin Najeriya.
Su dai wadannan mutanen sun bayyana cewa sun cika jikkunan su da guzuri sun kuma sha alwashin zuwa garin na Abuja a kasa domin nuna rashin jin dadin su game da yadda 'yan Najeriya ke shan bakar azaba kullu yaumin saboda rashin kyakkyawan shugabanci.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng