Kotu ta gargadi sanata Misau akan yin maganganu a kafofin watsa labarai
- Kotu ta umarci sanata Misau ya daina magana a kafofin watsa labaru akan laifufukan da ake tuhumar sa a kotu
- An sake gurfanar da Sanata Misau a gaban kotun tarayya akan yiwa sfeto janar na ‘yansanda karya da daganta shi da dabu'un banza
Babban kotun birnin tarayya dake, Maitama Abuja, ta gargadi sanata mai wakiltar mazabar Bauchi na tsakiya, Isah Misau, akan yin magana a kafofin watsa labaru akan game da laifufukan da ake tuhumar sa a kotu.
Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta sake gurfanar da Sanata Misau a gaban kotun akan yiwa sfeto janar na ‘yansanda, Ibrahim Idris kazafi da zargin cin hanci da rashawa da sauran su.

Lauyan Sanata, Misau, Mista Paul Erokoro (SAN), ya ce sanata ba zai kara yin magana a kafofin watsa labaru game da laifufukan da ake tuhumar sa ba.
KU KARANTA : Manoma miliyan 12m suka samu aikin yi a cikin wannan lokaci - Lai Mohammed
“Amma kada a manta shi sanata na mai wakiltar jama;a da yawa,” inji lauyan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng