Sauya fasalin kasa: Jam'iyyar APC tantiran mayaudara ne - Jam'iyyar adawa
Wata jam'iyyar adawa a Najeriya ta Action Democratic Party (ADP) ta yi fatali da rahoton gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya gabatar inda ya bukaci sake fasalin kasa tare da wasu sauye-sauye a makon da ya gabata.
Shugaban na jam'iyyar Action Democratic Party, dai mai suna Mista Yabagi Sani a yayin wata fira da yayi da manema labarai a garin Abuja ya bayyana rahoton a matsayin karin wata yaudara daga cikin kwarewar da jam'iyyar tayi.
KU KARANTA: Buhari yayi sassauci kan shigowa da abubuwa 36
Legit.ng ta samu cewa daga nan ne sai ya shawarci 'yan Najeriya da kada su bari jam'iyyar ta rude su da dadin baki irin yadda tayi a shekarar 2015 domin ta samu ta ci zabe.
A wani labarin kuma, Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun watau Osun Independent Electoral Commission a turance ta sanar da cewa jam'iyya mai mulki a jihar ta APC ta yi nasarar lashe dukkanin kujerun kansilolin jihar a zaben da aka gudanar a karshen satin da ya gabata.
Da ya ke ayyana sakamakon zaben, shugaban hukumar zaben ta Osun Independent Electoral Commission mai suna Mista Segun Oladitan ya bayyana cewa mutane 318 daga cikin su an sake zaben su ne ba hamayya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng