Taliban: Katoton bam ya fashe a Kabul babban birnin Afghanistan amma bai iya kashe kowa ba

Taliban: Katoton bam ya fashe a Kabul babban birnin Afghanistan amma bai iya kashe kowa ba

- Kabul babban birnin Afghanistan na shan hare-hare daga kungyoyin 'yan ta'adda shekaru da dama

- An kai hain ne a yau da safe a mota da aka makalawa bam

- Kungiyoyi masu zazzafan kishin Islama suna son kai hari wuraren da mutane kan shakata da sunan jihadi

Katoton bam ya fashe a Kabul babban birnin Aghanistan amma bai iya kashe kowa ba
Katoton bam ya fashe a Kabul babban birnin Aghanistan amma bai iya kashe kowa ba

A dazu da safe ne, wani bam da aka dana a mota ya tashi a wurin shakatawar jama'a a babban birnin Afghanistan a sabon hari da ake sa rai kungiyar Taliban ta kaishi domin kashe mutane.

Taliban: Katoton bam ya fashe a Kabul babban birnin Afghanistan amma bai iya kashe kowa ba
Taliban: Katoton bam ya fashe a Kabul babban birnin Afghanistan amma bai iya kashe kowa ba

Sai dai anyi sa'a bam din bai kashe kowa ba, sai dai ya raunata mutane da dama. Wannan kuma na zuwa ne bayan wani hari makamancin wannan a birnin a makon jiya a wani katafaren otal wanda ya kashe mutane 5.

DUBA WANNAN: Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen almajirta

Su dai rin wadannan hare-hare, ka iya hana baki masu zuba jari zuwa cikin kasar, da ma kuma jefa zullumi a zukatan mutane masu sha'awar walwala.

An fara irin wannan hare-hare ne tun bayan da Amurka ta kai wa kasar hari bayan hare-hare da aka kai mata wanda aka gano Usama bin Laden ne ya kitsa shi.

An kashe mutane da dama a yake-yake da kasar ke ciki tun mamayen tarayyar sobiyet a kasar, shekaru kusan 40 da suka wuce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel