An saka motar hawan Rooney a kasuwa

An saka motar hawan Rooney a kasuwa

- An saka motar shahararren dan wasan kwallon kafar kasar Ingila, Wayne Rooney, a kasuwa

- Ya ce zai yi amfani da kudin motar ne domin taimakon nakasassu

- Hukumomin kasar Ingila sun haramtawa Rooney tukin mota na shekaru biyu

An saka motar tsohon dan wasan kungiyar kwallo ta Manchester United dake taka leda yanzu a kungiyar kwallo ta Everton, Wayne Rooney, a kasuwa.

Motar dan wasan kirar BMW i8 da ya saya a shekarar 2015 a kan kudin kasar Ingila, fam 112,000, yanzu ya saka ta a kkasuwa a kan kudi fam €64,995 kamar yadda wakilin dan wasan ya sanar ga manema labarai.

An saka motar hawan Rooney a kasuwa
Wayne Rooney

Ko a lokacin da Rooney ya koma kungiyar kwallon kafa ta Everton daga Manchester United, a cikin motar ya isa filin da kungiyar ke taka leda domin ganawarsa ta farko da manema labarai.

DUBA WANNAN: Namun daji na fuskantar barazanar karewa a dazukan nahiyar Afrika

Dan wasan da hukumomi a kasar Ingila suka haramta wa tukin mota na tsawon shekaru saboda laifin kwankwadar barasa, ya ce zai yi amfani da kudin motar wajen tallafawa gidajen gajiyayyu a garin Liverpool, inda yake da zama yanzu.

Rahotanni sun bayyana cewar ko a wasu kwanaki da suka wuce saida Rooney ya bayar da tallafin makudan kudi ga wani gidan gajiyayyu dake wani kauye tare da yin kira ga ragowar 'yan kwallon kafa da suke taimakon masu karamin karfi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel