Labari mai dadi: Najeriya ta samu karin sabuwar matatar mai

Labari mai dadi: Najeriya ta samu karin sabuwar matatar mai

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni ne da cewa yanzu haka dai kasar Najeriya ta samu matatar mai irin ta saman ruwa mallakin kamfanin man nan na Total.

Wannan dai ya samu tabbatuwa ne bayan isowar wata matatar mai ta samn ruwa mai yawo da ka iya tace gangar danyen mai dubu dari biyu a kowace rana watau dai Floating Production Storage Offloading (FPSO) vessel a turance.

Labari mai dadi: Najeriya ta samu karin sabuwar matatar mai
Labari mai dadi: Najeriya ta samu karin sabuwar matatar mai

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya tattauna da jami'an hukumomin tsaro

Mun samu dai cewa matatar man an kiyasar kudin ta da suka kai $3.3 biliyan kuma ta taho ne daga kasar Koriya ta kudu inda aka kera ta kimanin watanni uku da suka gabata.

Legit.ng ta samu dai cewa yanzu za'a cigaba da aikin kammala hada ta da wasu rijiyoyin mai mallakin kasar dake a cikin teku kafin daga bisani ta fara aiki gadan-gadan .

Haka zalika mun samu cewa ana sa ran zuwan na wannan matatar man zai kawo karshen wahalar man da kasar ke fama da shi a wasu lokunan.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan kasar Tanzania ta nahiyar Afrika ta sanar da samun nasarar cafke akalla daliban Sakandare biyar a kasar dukkan su dauke da juna biyu inda a halin yanzu suke taimakawa jami'an tsaron domin gano iyayen su.

Jami'an tsaron dai sun shaidawa manema labarai cewa wadanda aka kama din dalibai ne da ba su wuce shekaru 16 zuwa 19 ba a duniya. Haka zalika sun bayyana cewa babban dalilin su na kama daliban shine domin yaki da yawaitar ciki barkatai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng