Satar Naira 400 miliyan: Kotun daukaka kara ta sha alwashin garkame Metuh

Satar Naira 400 miliyan: Kotun daukaka kara ta sha alwashin garkame Metuh

Wata kotun daukaka kara mallakin gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Abuja ta sha alwashin sai ta garkame tsohon kakakin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a takaice watau Olisa Metuh idan dai har bai gurfana a gaban ta ba ranar 5 ga watan Fabrairun shekarar nan.

Babban alkalin kotun ne dai mai shari'a Okon Abang ya sanar da hakan yayin da yake yanke hukunci game da uzurin da shi Olisa Metuh din ya gabatar ma kotun yana bukatar a sake daga shari'ar sa.

Satar Naira 400 miliyan: Kotun daukaka kara ta sha alwashin garkame Metuh
Satar Naira 400 miliyan: Kotun daukaka kara ta sha alwashin garkame Metuh

KU KARANTA: Wani fasto zai dauki nauyin koyawa almajirai sana'a

Legit.ng ta samu cewa sai dai alkalin kotun ko kusa bai ji dadin yadda yake kokarin yin wasa da hankalin su ba inda kuma ya bayyana rashin gamsuwa game da uzurin nasa.

A wani labarin kuma, Labarin da muke samu yanzu-yanzu na nuni da cewa an rufe filin sauka da kuma tashin jiragen sama na kasa-da-kasa na tunawa da Nnamdi Azikwe dake a garin Abuja.

Mun samu dai cewa an rufe filin jirgin ne na dan wani lokaci biyo bayan wata 'yar tangarda da wani jirin yawo mallakin kamfanin Nest Oil ya samu yayin da yake kokarin sauka a yau din nan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Online view pixel