An kama babban faston Najeriya a kasar Zambia kan laifin safaran miyagun kwayoyi
Wani mai magana da yawun hukumomin kasar Zambia a ranar Alhamis ya sanar da cewa, hukuma ta kama wani faston Najeriya da laifin safarar miyagun kwayoyi da kwayoyin kara kuzari kilo 26.29.
Fasto Isaac Amata, dan shekaru 42, sananne ne don hasashe da yayi na cewan Shugaban kasa Edgar Langu zai yi nasara a zaben kasar Zambia a 2016.
A cewar mai magana da yawun hukumar dake yaki da miyagun kwayoyi, Theresa Katongo, jami’an hukumar sun kama shi ne a ranar Laraba bayan ya sauka a filin jirgin sama na Kenneth Kaunda dake Lusaka, babban birnin tarayyar kasar.
Ta ce an kama faston ne bayan saukar shi a filin jirgin sama daga Najeriya a jirgin sama na Kudancin Afurka.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Evans, biloniyan dake garkuwa da mutane ya kai karan yan sanda kan kwace masa manyan motocin daukar kaya 25
Ta ce a halin yanzu mai laifin yana a hannun yan sanda kuma zai gurfana a kotu nan ba da dadewa ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=
Asali: Legit.ng