Rundunar sojin sama ta kulla wata yarjejeniya da kamfanin kera kayayyaki na Najeriya (hotuna)
Rundunar Sojin Sama a jiya 24 ga watan Janairu 2018, ta sa hannu a yarjejeniya tare da kamfanin kayan aikin na’ura na Najeriya a Osogbo duk a cikin kokarinta na ganin ta karfafa al’adan dogaro da kanta.
Wannan yarjejeniyar har ila yau yana da manufar cigaban tarayyar dabarun rundunar tare da ma’aikata da hukumomi ta hanyar inganta bincike da cigaba.
Daga cikin yarjejeniyar da ta kulla sun hada da horarwa, kera na’ura, kirkirawa, gyare-gyare tare da bincike da kuma kawo cigaba.
KU KARANTA KUMA: Hukumar INEC zata dakatar da yin rijista kwanaki 60 kafin zaben 2019
Yarjejeniyar ta shafi fannin ci gaba da samar ma hafsoshinta kayan sufuri da kayan kariya na jirgin sama.
A wajen bikin yarjejeniyar, wanda aka gudanar a harabar hedikwatar Rundunar a Abuja, babban manajan kamfanin na’urar, Mista Nobert Chukwuma, ya bayyana farin ciki bisa dama da aka ba kamfanin don hada kai tare da rundunar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng