Kungiyar 'yan tawayen da ke yiwa gwamnatin Libya biyayya sun kama mutanen dake azabtar da ‘yan gudun hijira

Kungiyar 'yan tawayen da ke yiwa gwamnatin Libya biyayya sun kama mutanen dake azabtar da ‘yan gudun hijira

- Kungiyar 'yan tawayen da ke yiwa gwamnatin Libya biyayya sun ceto 'yan gudun hijira guda takwas daga hanun masu fataucin dan Adam

- Masu fataucin dan Adam a kasar Libya suna kona duk dan gudun hijiran da ya kasa biyan kudin fansa ran sa

Kungiyar 'yan tawayen da ke yiwa gwamnatin hadin gwiwa na kasar Libya biyayya ta ce ta kama gugun masu fataucin dan Adam da ake zargin su da yin garkuwa da azabtar da' yan gudun hijira daga kasar Sudan, a kusa da birnin Sirte.

Maus laifin da aka kama ya hada da ‘yan kasar Libya guda biyar da mutum daya daga kasar Filastine, sun azabtar da ‘yan gudun hijira guda takwas a lokacin da aka kama su inji jami’an tsaron birnin Sirte.

An garzaya da ‘yan gudun hijira zuwa asibitin Ibn Sina dake birnin Sirte dan duba lafiyar su.

Kungiyar 'yan tawayen da ke yiwa gwamnatin Libya biyayya sun kama mutanen dake azabtar da ‘yan gudun hijira
Kungiyar 'yan tawayen da ke yiwa gwamnatin Libya biyayya sun kama mutanen dake azabtar da ‘yan gudun hijira

An kama masu laifin ne a kauyen Qaddahiya dake kusa da kudancin birnin Sirte, bayan wani bidiyo da ya nuna yadda su ke azabatr da ‘yan gudun hijira a shafukan sa da zumunta.

KU KARANTA : APC ta mayar da martani game da wasikar Obasanjo zuwa Buhari

Bidiyon ya nuna yadda ake kona ‘yan gudun hijiran da basu da kudin fansa kan su bayan anyi garkuwa da su.

Kungiyar ‘yan tawayen dake yiwa gwamnatin Libya biyayya sun ce an saki ‘yan gudun hijira guda takwas da suke ceto.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng