Tsagerun Neja Delta sun ba Fulani wa’din wata daya su bar yankin su
- 'Yan tawayen Neja Delta sun ba Fulani makiyaya kwanaki 90 su bar yankin su
- Gamayyar kungiyar 'yan tawayen Niger Delta sun ce za su kafa gwamnatin jamhuriyyar Neja Delta idan gwamnati ta kasa biyan bukatan su
Kungiyar 'yan tawayen Neja Delta sun gargadi Fulani makiyayan akan zuwa yin kiwo a yankin su
Gamayyar kungiyar 'Yan tawayen Niger Delta sun yi wannan gargadin ne a ranar Laraba a birnin Fatakol inda suka lissafo adadin bututun man da za su fasa idan gwamnatin tarayya ta kasa biyan bukatun yankin su.
Kungiyoyin ‘yan tawayen da suka sanya hannu akan wannan yarjejeniyar, sun hada da John Duku na kungiyar (CNDA), Ekpo Ekpo na kungiyar (NDV), Osarolor Nedam na kungiyar (NDW) da Simply Benjamin na kungiyar (BSF).
'Yan tawayen sun ba gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 90 ta sauya fasalin kasar ta inda kowace jiha zata rika kula da arzikin ta, da maida rijiyoyin mai zuwa hannun mutanen Neja delta da kuma dawo da duka shelkwatar kamfanonin mai yankin.
KU KARANTA : APC ta mayar da martani game da wasikar Obasanjo zuwa Buhari
Sun ce, “In ba haka babu Najeriya daya. Zamu kafa gwamnatin jamhuriyyar Neja Delta nan da kwanako 90, idan gwamnati ta kasa aiwatar duka bukatun da muka lissafo.
“Kuma muna ba duka mutanen Arewa dake zama a yankin Neja Delta wa’adin barin yankin mu idan gwamnatin tarayya ta kasa biyan bukatun mu.
“Kuma muna kiran mutanen mu dake zama a Arewa su gaggauta dawowa Neja Delta saboda lafiyar su
Bututun man da za mu fasa sun hada da bututun man dake Usan, Ima, Okoro/Setu, Asabo, Exxon Mobil, Chevron, Intels, Adax, da kamfanin Total.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng