Wasikar Obasanjo: Wannan rashin mutunci ne, ya sabawa tunani – Farfesa Itse Sagay
Shugaban kwamitin fadar shugaban kasa kan bada shawara akan rashawa, Farfesa Itse Sagay ya ce rashin mutunci ne tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya cewa shugaba Muhammadu Buhari kada yayi takara zaben 2019.
Sagay ya yi kira ga Obasanjo wanda ya bukaci yin tazarce ya nuna girma ga shugaba Buhari.
Yace: “Na ga maganganun Obasanjo kuma abin ya bani mamaki, mutumin da yayi kokarin tazarce karo na uku amma yana cewa wani kada ya sake neman takara. Wannan abu ya sabawa hankali.
“Ya kamata Obasanjo yayi kokari ya ga mutuncin mutane. Ya yi nasara sosai, babban mutum ne kuma ina girmama shi. Amma ya koyi girmama wasu.”
“Ina ganin rashin mutunci ga mutumin da ya bukaci tazarce na uku ya baiwa wanda ke neman tazarce na biyu wannan shawara. Wannan bai dace ba.”

Amma wani babban lauya kuma tsohon shugaba kungiyar lauyoyin Najeriya, Dr Olisa Agbakoba (SAN), ya ce babu abinda shugaba Buhari zai iya tsinanawa.
KU KARANTA: Jami’ar zata hukunta duk ɗalibin daya zazzago da wandonsa, da masu askin banza
Kana babban lauya, Femi Falana, ya siffanta wasikar Obasanjo a matsayin wa’azi ga shugaba Buhari. Ya bashi shawara ya kawar da miyagun da zagaye da shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng