Zuwan Kano: Manyan tsaffin sojoji da 'yan sanda za su ba Kwankwaso kariya

Zuwan Kano: Manyan tsaffin sojoji da 'yan sanda za su ba Kwankwaso kariya

Tsohown gwamnan jihar Kano kuma dan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar jihar Kano ta tsakiya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso ya nada kwamitin mutane 19 da za su tabbatar da samuwar tsaro yayin ziyarar da zai kai a jihar ta sa ta haihuwa ranar 30 ga watan Janairun nan da muke ciki.

Kwamitin tsaron dai kamar yadda muka samu ya samu shugabancin tsohon hafsan soji Janar Abdulrahman Bello Danbazau, minstan harkokin tsaron cikin gida yayin da Barista Munir Dahiru ya zama sakataren kwamitin.

Zuwan Kano: Manyan tsaffin sojoji da 'yan sanda za su ba Kwankwaso kariya
Zuwan Kano: Manyan tsaffin sojoji da 'yan sanda za su ba Kwankwaso kariya

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kama kanwar Patience Jonathan

Legit.ng ta samu cewa sauran mambobin kwamitin sun hada da Air Commodore Ali Bebeji, Air Commodore Zakari Baffa Colonel Usman Garun-Malam, Air Commodore Salisu Yusha’u, Major General Ahmad Tijjani Jibril, da kuma AIG Bala Abdullahi.

Haka zalika sauran sun hada da Commander Sarki Aliyu Daneji, Alhaji M.T Usman, Hon. Lawal Sale Gaya, Alhaji Baba Umar, Alhaji Tijjani Dambazau, CP Rabi’u Mani, Commander Kamilu Wudil, Alhaji Sanusi Surajo Kwankwaso, Alhaji Adamu Garko da kuma Alhaji Muhammad Ado Danbatta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng