Bambarakwai: Sabuwar Amarya ta kashe jaririyarta kwana guda da haihuwa

Bambarakwai: Sabuwar Amarya ta kashe jaririyarta kwana guda da haihuwa

Rundunar Yansandan jihar Jigawa ta cafke wata mata mai shekaru 25, Hadiza Danfanna biyo bayan hallaka yaronta, jaririyar yan kwana daya da haihuwa, da tayi.

Daily Trust ta ruwaito Hadiza ta yi aure ne alhalin tana dauke da ciki wata hudu, kuma a haka ta boye cikin har zuwa lokacin da ta haihu, ba tare da mijinta ya sani ba,sa’annan ta jefar da jaririyar.

KU KARANTA: Ke Duniya: Al’adar wasu ƙauyawa dake kashe ýan biyu da Zabiya a babban birnin tarayya Abuja

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tsohon saurayin Hadiza mai suna Lili ne ya dirka mata wannan ciki, kafin ta yi aure, hakan ne ya sanya ta kasa fada ma mijinta halin da ake ciki, har sai da ta haihu, ta jefar da jaririn, sa’annan asirinta ya tonu.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar Jigawa, ASP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma yayi Karin haske, inda yace Hadiza ta jefar da jaririn ne a wani filin kwallo, da warin gawar ya addabi yan kwallon ne sai suka shiga neman abinda ke wari, har suka ci karo da gawar tana rubewa.

“Mun kama Hadiza da Lili, kuma da zararan kammala bincike, zamu gurfanar dasu gaban Kotu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng