Akwai ‘yan gudun hijira 10,000 daga kasa Kamaru a Najeriya – Majalissar Dinkin Duniya (UN)
- UN ta bayyana damuwarta akan irin kunci rayuwan da 'yan gudun hijira daga kasar Kamaru ke fuskanta
- Kungiyar UNCHCR ta zata hada kai da hukumomi a Najeriya dan taimakawa 'yan gudun hijiran kasar Kamaru dake neman mafaka a Najeriya
Majalissar Dinkin Duniya UN ta bayyana damuwar ta akan yadda ‘yan yankin dake amfani da harshen turanci a kasar Kamaru suke guduwa zuwa Najeriya dan neman mafaka, musamman mata da kananan yara.
Mai magana da yawun bakin kungiyar kula da ‘yan gudun hijira dake karkashin majalisar Dinkin Duniya (UNCHCR), William Spindler, yayi korafi akan irin kunci rayuwan da mata da kananan yara suke fuskanta a sansanin yan gudu hijira a Najeriya.
Anyi rijistan ‘yan gudun hijira daga kasar Kamaru guda 10,000 a jihar, Cross Rivers wanda kashi 80% daga cikin su mata da kananan yara ne.
Kungiyar UNHCR sun ce, sun samu rahotanni da suka nuna kananan yara suna yin aiki ko bara kafin su abincin ci da tallafawa iyayen su.
KU KARANTA : Zaben 2019: Na ga Buhari a matsayin shugaban kasa, Atiku zai fadi - Fasto Ayodele
Kuma basa zuwa makaranta saboda rashin kudi da lokaci.
UNHCR ta na aiki da hukumomin Najeriya wajen ganin an taimaki ‘yan gudun hijiran.
Tun a watan Yuni na shekara 2017 ‘yan Yankin dake amfani da harshen turanci a kasar Kamaru wanda aka fi sani da Anglophone suka fara zanga-zanga akan bambanci da gwamnatin ke nuna wa a tsakanin su da masu amfani da yaran Faransa a kasar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng