'Yansada sun kama mutane biyu da naira miliyan N8m na jabu a jihar Neja

'Yansada sun kama mutane biyu da naira miliyan N8m na jabu a jihar Neja

- Rundunar 'yansanda jihar Neja ta kama masu buga jabun kudi a Suleja

- 'Yansanda sun samu bindgar toka, adda da naira miliyana N8m daga hanun masu buga kudin jabu a Suleja

Rundunar ‘yansadar jihar Neja ta ce takama naira mIliyan N8m na jabu daga hanun, wani Abdulkharim Adamu, mai shekaru 70 da Umar Auta mai shekaru 50.

‘Yansada sun kama Adamu da Auta ne a wata tsohuwar kwata dake Suleja a makon da yagabata.

Mai magana da yawun bakin rundunar ‘yansandar jihar Neja, ASP Mohammed Abubakar ya fadawa manema labaru cewa sun sun samu bindigan toka, adda a cikin gidan da masu laifin ke zama.

'Yansada sun kama mutane biyu da naira miliyan N8m na jabu a jihar Neja
'Yansada sun kama mutane biyu da naira miliyan N8m na jabu a jihar Neja

ASP Abubakar, yace binciken da suka gudanar ya nuna masu laifin sun dade suna sana’ar buga jabun kudade.

KU KARANTA : Jihohi 16 sun shirya ba gwamantin tarayya hadin kai wajen kaddamar da shirin samar wa makiyaya filayen kiwo - Olukayode

Abubakar yace masu lafin sun amsa lafin su, kuma sunce sunyi nadama kuma, amma za mu kai su kotu dan a gurfanar da su.

ASP Mohammed Abubakar, yayi gagardi da cewa, babu wajen boya ga mabarnata a jihar Neja, kuma su cigaba da farautan su dan dan tabbatar ingantaccen tsaro ya samu a jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng