Lokaci yayi da shugaba Buhari zai yi murabus daga muƙamin Ministan man fetir na kasa

Lokaci yayi da shugaba Buhari zai yi murabus daga muƙamin Ministan man fetir na kasa

Jigo a cikin jam’iyyar APC, Alhaji Muhammad Ibrahim Daura ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi wa Allah ya saki mukamin ministan man fetir da a yanzu yake rike da shi.

Daura ya bayyana haka ne a wata ganawa da yayi da manema labaru a Kaduna, inda yace kamata yayi Buhari ya hakura da ministan, ya fuskanci al’amuran mulki ta yadda ya dace, sa’annan yayi ga Buhari daya sake tsayawa takara, duba da kyawawan ayyukan da ya fara, don ganin ya kammala su.

KU KARANTA: Mulki sai da lissafi, don haka ba’a raba ni da Kalkuleta – Inji Gwamnan jihar Jigawa

Daily Trust ta ruwaito jigon yana fadin ma’aikatar man fetir na da matukar muhimmanc, don haka ya dace Buhari ya mika ta gam asana, su zasu tafiyar da ita yada ya kamata, inda yace tun bayan zamansa shugaban kasa, Buhari bait aba zagaya matatun man Najeriya ba, balle ya san abinda ya dace dasu.

Lokaci yayi da shugaba Buhari zai yi murabusa daga muƙamin Ministan man fetir na kasa
Buhari
Asali: Facebook

“Bugu da kari, shi kansa karamin minstan mai, Ibe Kachikwu, Lauya ne, don haka ba lallai ne ya san dabarun sarrafa al’amuran mai ba, duba da cewa mai ne ke samar ma Najeriya kaso mai tsoka na kudaden shiga, ya zama wajibi a bata muhimmanci, kafin ta haifar mana da matsala.” Inji shi

Daga karshe Daura ya shaida ma majiyar Legit.ng cewa karancin mai da ake fama da shi nada nasaba da yadda Buhari ke tafiyar da ma’aikatan man fetir daga fadar shugaban kasa, hakan bai dace ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng