Yadda dukan wasu dalibai ya yi sanadin dakatar da shugaban makaranta da malamai biyu

Yadda dukan wasu dalibai ya yi sanadin dakatar da shugaban makaranta da malamai biyu

- An dakatar da shugaban wata makaranta da wasu malamai biyu saboda dukan wasu dalibai

- An dakatar da su daga aikin ne saboda sun saka faifan dukan daliban a yanar gizo

- Ma'aikatar ilimi ta ce abin da malaman suka yi ya jawo mata abin kunya

Gwamnatin jihar Nasarawa ta dakatar da shugaban wata makarantar sakandire dake Nasarawan Eggon da karin wasu malamai biyu saboda zartar da hukunci mai tsanani a kan wasu dalibai da su ka dawo makarantar a makare.

Shugaban makarantar da malaman biyu sun watsa faifan bidiyon hukuncin da suka zartar a kan daliban a yanar gizo, lamarin da ma'aikatar ilimin jihar ta ce ya jawo mata abin kunya.

Yadda dukan wasu dalibi ya yi sanadin dakatar da shugaban makaranta da malamai biyu
Yadda dukan wasu dalibi ya yi sanadin dakatar da shugaban makaranta da malamai biyu

A wata ganawa da ya yi da manema labarai, kwamishinan ilimin jihar Nasarawa, Tijjani Aliyu Ahmed, ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta dakatar da shugaban makarantar tare da kafa kwamitin bincike a kan lamarin. Kazalika, kwamishinan ya jaddada cewar yin hukunci mai tsanani ga dalibai ya sabawa dokar aikin koyarwa a jihar.

DUBA WANNAN: Ku kalli yadda gwamnatin jihar Sokoto ta yi ruwan kayan aiki ga makarantun jihar

"Da kun kalli faifan bidiyon zaku fi fahimtar abinda nake nufi, abinda suka yi ga daliban zalunci ne. Mun dakatar da shugaban makarantar, da malami mai kula da dakin kwanan dalibai, da kuma malamin da ya watsa faifan bidiyon a yanar gizo," a cewar Amhed.

Ahmed ya bayyana cewar mataimakin shugaban makarantar zai cigaba da tafiyar da al'amuran koyarwa a matsayin rikon kwarya.

Saidai, shugaban makarantar na rikon kwarya, Umaru Kasimu, ya ki furta komai yayin da manema labarai suka nemi jin ta bakinsa.

A wani labarin mai alaka da wannan, kwamishinan ya bayyana cewar ma'aikatar ilimin jihar ta dakatar da babban sakataren hukumar bayar da tallafi, Abdulwahab Suleiman. Ya ce an dakatar da shine saboda jinkirin hukumar da yake jagoranta wajen rabon gadajen kwanciyar dalibai da gwamnati ta samar ga makarantun jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng