Harsashin wasu ma'aikatan kwastam akan aiki ya rutsa da wata mai ciki

Harsashin wasu ma'aikatan kwastam akan aiki ya rutsa da wata mai ciki

- Harsashi ya sama wata mata mai ciki, wanda wani jami’in fasa kauri ya harba a iska da niyyar ya tarwatsa ‘yan zanga zanga

- Abin ya faru a ranar alhamis din nan garin Ota, dake jihar Ogun, wanda yasa aka garzaya da matar asibiti. Matar wadda aka fi sani da Mrs. Ogunlana

Harsashin wasu ma'aikatan kwastam akan aiki ya rutsa da wata mai ciki
Harsashin wasu ma'aikatan kwastam akan aiki ya rutsa da wata mai ciki

Wani wanda abin ya faru a gaban shi ya shaidawa majiyar mu cewar, matar wanda take dauke da ciki har na tsawon wata takwas, ibtila’in ya faru da ita a dai dai lokacin da wani jami’in fasa kauri ya harba harsashi cikin iska da niyyar ya tarwatsa ‘yan zanga-zanga da suke kokarin hana su kama wani direba.

Mrs. Ogunlana, wanda take aiki da kamfanin wutar nefa dake Ibadan, harsashin ya sameta a kafadar ta. Wanda yanxu take karbar magani a asibiti.

Da yake jawabi akan al’amarin, mai magana da yawun shugaban ‘yan fasa kaurin, dake Jihar Legas, Jerry Attah yace matar tana nan cikin koshin lafiya. Ya tabbatar da cewar sun kira shugaban yan fasa kaurin mai kula da hiyyar inda ya tabbatar da cewar lamarin ya faru, amma an garzaya da matar asibiti. Sannan hukumar fasa kaurin zata dauki nauyin kudin maganin ta. Yayi godiya ga Allah da yasa abin bai kai ga an rasa rai ba.

Wannan mummunan al’amarin ya faru kwana daya bayan da wani jami’in fasa kauri ya kashe wani yaron mota. Hukumar fasa kaurin ta samu rahoton wata mota dauke da shinkafa wanda aka shigo da ita ta barauniyar hanya. A kokarin su na ganin sun kama direban motar, ‘yan zanga zangar sun yiwo kan jami’in fasa kaurin, wanda yasa shi harbi cikin iska, harbin da yayi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin ‘yan zanga zangar. Inda su kuma hukumar fasa kaurin suka musunta faruwan hakan.

Yayinda yake jawabi Mr. Attah yace mutane sun fusata shine yasa suke so suyi amfani da abinda ya faru yau suke yada jita-jitar cewar matar ta mutu.

A halin yanxu dai ‘yan sanda sun tafi da jami’in fasa kaurin ofishin su domin gudanar da bincike.

[2:21 PM, 1/18/2018] +234 803 288 0989:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng