Rikicin Makiyaya: Majalisar Wakilai tayi kira ga NEMA da ta kai kayan agaji ga jigatattu a jihohin Benue da Nassarawa

Rikicin Makiyaya: Majalisar Wakilai tayi kira ga NEMA da ta kai kayan agaji ga jigatattu a jihohin Benue da Nassarawa

Tun bayan da hare-haren makiyaya wanda ake dangantawa da Fulanin daji, wanda ya kashe da dama a kauyuka a jihar Binuwai, da Nassarawa, jama'a da yawa sun bazama daji, wasu kuwa sun koma zama a sansanonin 'yan gudun hijira, wandanda gwamnati ta kafa

Rikicin Makiyaya: Majalisar Wakilai tayi kira ga NEMA da ta kai kayan agaji ga jigatattu a Benue
Rikicin Makiyaya: Majalisar Wakilai tayi kira ga NEMA da ta kai kayan agaji ga jigatattu a Benue

A ranar laraban nan ne majalisar wakilai ta kasa ta bukaci NEMA, ta ba da kayan agaji ga sansanin ‘yan gudun hijira dake Awe, Azara, Keana da Rukubi dake cikin jihar Nasarawa. Sun bukaci a kai abinci, magunguna, ruwan sha da sauran su.

DUBA WANNAN: An sace BA-Amurke a Kaduna

Mohammed Ogoshi Onawo shi yayi wannan kiran yayin da yake jawabi, ya bayyana cewa rikice rikicen dake tsakanin yankunan Tiv, da kuma fulani makiyaya, wanda yayi sanadiyyar al’ummar wurin suka bar gidajen su.

Ya ce rikicin yayi sanadiyyar rayuka da dukiyoyi wanda ya tilasta wa mazauna wurin neman mafaka a yankin Awe, Keana, da Doma dake jihar Nasarawa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel