Toh fa! An zargi wani Ministan Buhari da ɗaukan nauyin gungun yan ta’adda

Toh fa! An zargi wani Ministan Buhari da ɗaukan nauyin gungun yan ta’adda

Karamin ministan harkan noma da cigaban karkara, Sanata Heinekn Lokpobri ya musanta zargin da gwamnatin jihar Bayelsa ta yi masa na cewa wai shine ke daukan nauyin wani kasurgumin dan ta’adda.

Minista Lokpobri ya ce ba shi da hannu cikin daukan nauyin wannan dan ta’adda, daya daga cikin jiga jigan tsagerun Neja Delta dake tayar da kayar baya a yankin, mai suna Peregbakumo Oyawerikumo, mai inkiya Karowei.

KU KARANTA: Tsadar rayuwa da baƙin talauci ya sanya Magidanci hallaka iyalinsa gaba ɗaya, da shi kansa

Daily Trust ta ruwaito gwamnan jihar Bayelsa, Sariake Dickson yana danganta ministan da wannan dan ta’adda, wanda a yanzu haka an kashe shi da ministan tare da tsohon gwamnan jihar, Timipre Sylva, inda ya roki shugaban kasa Buhari da ya ja kunnensu akan su daina daukan nauyin yan ta’adda.

Toh fa! An zargi wani Ministan Buhari da ɗaukan nauyin gungun yan ta’adda
Minista

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin ganawar da yake yi da manema labaru a duk wata, inda yace rahotannin sirri sun tabbatar da cewar a ranar 3 ga watan Janairu, Ministan yana tare da Karowei.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito Ministan cikin wata sanarwar daya fitar yana musanta batun, inda yace ba shi da wata alaka da dan ta’addan ko kuma wasu gungun yan ta’adda, balle kuma a yi batun wai yana basu makamai.

Ministan ya tabbatar da cewar an yi bikin shiga sabuwar shekara da shi a kauyensu, Ekeremor, amma a ranar 2 ga watan Janairu ya bar garin, inda yace a ranar 31 ga watan Janairu Karowei ya same shi da tare gungun yaransa, inda suka yi masa barazanar kashe shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng