Da zafi-zafi: Gwamnatin tarayya ta biya N450b kudin tallafin mai – Sanata Marafa

Da zafi-zafi: Gwamnatin tarayya ta biya N450b kudin tallafin mai – Sanata Marafa

- Majalisar dattawa ta tattauna da ministan mai da manajan NNPC a kan abinda ya jawo wahalan man fetur

- A zaman, karamin ministan mai, Kachikwu, ya bayyana cewa har ila yau suna biyan tallafi

- Duk da hakan kuma, mutane basu daina wahalan samun man fetur ba

Shugaban kwamitin majalisan dattawa akan man fetur, Sanata Kabiru Marafa, a yau Laraba, 17 ga watan Junairu ya bayyanawa abokan aikinsa da yan Najeriya cewa zuwa yanzu gwamnatin tarayya ta biya N450 biliyan kudin tallafin man fetur

Sanata Marafa ya ce kamfanin man fetur ta kasa, NNPC ce ta biyya wannan kudi ba tare da ilimin majalisa ba kuma wannan ya sabawa doka.

Da zafi-zafi: Gwamnatin tarayya ta biya N450b kudin tallafin mai – Sanata Marafa

Da zafi-zafi: Gwamnatin tarayya ta biya N450b kudin tallafin mai – Sanata Marafa

Ya ce shugaba Muhammadu Buhari wanda shine ministan mai ne ya bada izinin biyan wannan kudi.

KU KARANTA: Rundunar soji zata canja tsarin tura dakarunta yankin Arewa maso gabas – Inji Buratai

Za ku tuna cewa a watan Mayu na shekarar 2016, gwamnatin tarayya da kara kudin litan man fetur daga N85 zuwa N145 da hujjan cewa ta janye tallafin man fetur kuma ba za’a kara samun wahalan mai ba, amma angulu ta koma gidanta na tsamiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel