Wata matashiya ta dau alwashin halaka duk mijin da ya yi mata kishiya

Wata matashiya ta dau alwashin halaka duk mijin da ya yi mata kishiya

Ta tabbata yayin da shuwagabanni ke ganin matsalar matasan Arewa ya ta’allaka ne kadai ga matsalar shaye shaye, ashe an yi tuya ne aka manta da albasa, kamar yadda zaku gani cikin wannan bidiyon.

A nan wata budurwa ce mai tsananin rashin kunya, ta sha alwashin hallaka duk mijin daya auro mata kishiya, ‘don kuwa ni fa ba ni da imani’ inji fitsararriyar, kamar yadda Legit.ng ta gano.

KU KARANTA: Tsadar rayuwa da baƙin talauci ya sanya Magidanci hallaka iyalinsa gaba ɗaya, da shi kansa

Wannan budurwa da ba’a bayyana sunanta ba ta bayyana hakane yayin da take hira da wasu samari guda biyu, wanda suka dauke ta wayar ta yayin da take ta sakin baki, sai dai hirar tayi kama da irin hirar da matasa suka saba yi a tsakaninsu.

A yayin hirar, matashiyar ta bayyana ba zata daga ma duk mijin da yayi mata kishiya kafa ba, inda ta bayar da labarin wani saurayinta da sabuwar budurwar da yayi, yadda ta same su suna zaune suna hira, ita kuma ta caccaka ma yarinyar makullai a fuska, bayan ta fasa mata waya, sa’annan ta zazzagi saurayin.

Ga dai bidiyon nan ga mai sha’awar kallo:

Da fatan zai zama izina ga iyaye da shuwagabanni, don ganin cewa an tashi haikan kan kula da tarbiyyar yaran mu na Arewacin kasar nan, musamman ma Musulmai, don kuwa idan al’umma ta lalace, babu wanda zai sha.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng