Ku zamo masu hakuri a tsakaninku – Sakataren tarayya ga yan Najeriya
- Babban sakataren tarayya ya shawarci yan Najeriya da su zamo masu hakuri
- Boss Mustapha ya bayyana hakan a matsayin hanya guda da zai kawo ci gaba a kasar
- An yabi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zabar Mustapha da yayi a matsayin Sakataren gwamnatin tarayya
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bukaci yan Najeriya da su guji duk wasu abubuwa da zasu kawo rabe-raben kai a tsakaninsu sannan su rungumi kadaici kan manufar cigaban kasa.
Sakataren ya bayyana hakan ne a wani jawabin da ya yi a Abuja a karshen mako da ya gabata a wani taron liyafa da abokai suka hada don daraja shi.
“Najeriya da muka sani a da bata nuna mana rabe-rabe ba, tashin hankali da rigingimu ba, a halin yanzu ta kasance tare da al’amura marasa kyau. Idan bamu tashi cikin gaggawa ba, baza mu wasiyyanci wannan Najeriya ga yayanmu ba da zuriyarsu. A shekaru aro-aro da suka gabata, mun bari al’adan rabe-rabe ya girma tsakaninmu sosai har ya kai ga abokantaka, hulda da zumunci tare da sauran mutane, a halin yanzu sai an kafa sharadin kabila ko addini da ka kasance ciki”. Inji Mustapha
KU KARANTA KUMA: Wani Sanatan Katsina ya gargadi Buhari akan kafa burtalin makiyaya a jihohi
Shugaban ma’aikata na kasa Misis Winifred Oyo-Ita da ministan babban birnin tarayya Mallam Musa Bello sun yabi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zabin Mustapha da yayi a matsayin Sakataren gwamnatin tarayya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng