Al’amarin Najeriya bai fi karfin Buhari ba – Kungiyar BSO

Al’amarin Najeriya bai fi karfin Buhari ba – Kungiyar BSO

- Kungiyar BSO ta ce tunda Buhari ya zama shugaban kasar Najeriya aka samu cigaba a fannin tsaro

- Jagoran kungiyar BSO ya ce nasarar da gwamnatin Buhari ta samu wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar yasa ya cancacnci a kara zaben shi

Kungiyar nuna goyon bayan Buhari (BSO) ta ce an samu cigaba a fannin tsaro shekaru biyu da rabi bayan Muhammadu Buhari yazama shugaban kasar Najeriya.

Da yake jawabi a taron manema labaru a jiya Talata a jihar Katsina, jagoran kungiyar BSO, Ibrahim Kallah ya ce "cigaban da akam a fannin tsaro abun farin ciki ne” ganin yadda aka kare dukiyoyi da rayuka.

Al’amarin Najeriya bai fi karfin Buhari – Kungiyar BSO
Al’amarin Najeriya bai fi karfin Buhari – Kungiyar BSO
Asali: Depositphotos

Kallah ya ce” magance matsalar masu garkuwa da mutane a fadin kasar da kama jagororin da kuma rage karfin kungiyar Boko Haram a yankin Arewacin Najeriya abun murna ne da frin ciki.”

KU KARANTA : Gwamnatin jihar Nassarawa tace zataci gaba da taimakawa 'yan gudun hijira

Ya yayi kira da yan Najeriya su rika lura da kokarin da gwamnatin Buhari ta key i musamman wajen yakar yan kungiyar Boko Haam, kwato kananan hukumomi 14 daga hanun yan ta’dda da kuma ceto ‘yan matan Chibok 106.

Kallah yace, cigaba da zaman lafiya da ake yi a yankin Neja Delta ta cigaba da tallafawa tubabbun tsagerun Neja Delta abun yabawa ne da ya cancanci a kara zaben shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel