Dandalin Kannywood: Fati Muhammad ta sha alwashin auren wani malamin Islama

Dandalin Kannywood: Fati Muhammad ta sha alwashin auren wani malamin Islama

Sanannar jarumar nan a da ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood a shekarun baya watau Fati Muhammad ta bayyana aniyar ta na auren wani fitaccen malamin addinin Islama mai suna Mallam Datti Assalafi.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata budaddiyar wasika da ta rubutwa malamin a shafin ta na dandalin sada zumunta na Facebook a jiya Talata, 16 ga watan Janairu biyo bayan abun da ta kira cin mutuncin da yayi mata da kage da sharri.

Dandalin Kannywood: Fati Muhammad ta sha alwashin auren wani malamin Islama
Dandalin Kannywood: Fati Muhammad ta sha alwashin auren wani malamin Islama

KU KARANTA: Da cikakken goyon bayan iyaye na na fara harkar fim - Khadija Mustapha

Legit.ng dai ta samu cewa jarumar ta yi wa malamin budaddiyar wasika ne biyo bayan wani rubutu da yayi akan ta inda ya zarge ta da biyewa masu kudi da 'yan siyasa suna kwana da su domin samun kudi.

Sai dai jarumar ta bayyana hakan da yayi a matsayin abun takaici inda tace in ma har gyara ko nasiha yake so yayi mata to ba ta hanyar cin ya kamata yayi mata ba don ba zai yi wa kanwar sa ko diyar sa hakan ba.

Daga karshe sai jarumar ta bukaci malamin da ya fito ita kuma a shirye take da ta aure shi idan dai har da gaske yake yi so yake yi tayi aure.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Online view pixel