Mun rasa mambobi mu guda 1000 da shanu miliyan biyu - Makiyaya

Mun rasa mambobi mu guda 1000 da shanu miliyan biyu - Makiyaya

- Kungiyar makiyayan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta biya mambobin su da suka yi asara diyya

- Kungiyar MACBAN ta bukaci gwamnatin tarayya ta samar da ma'aikatan kula da harkokin makiyaya a Najeriya

Makiyayan dake karkashen kungiyar, Miyyeti Allah (MACBAN), sun ce sun rasa mambobi 1,000 da ya kunshi kananan yara da iyaye mata da kuma asarar shanu sama da miliyan biyu.

Sakataren kungiyar MACBAN na kasa, Alhaji Baba Ngelzarma, wanda yayi jawabin a madadin makiyaya, yayi kira da gwamnatin tarayya ta taimaka ta biya mambobin su da suka yi asarar dukiyoyin su ta sanadiyar rikici diyya.

Mun rasa mambobi mu guda 1000 da shanu miliyan biyu - Makiyaya
Mun rasa mambobi mu guda 1000 da shanu miliyan biyu - Makiyaya

Alhaji Baba Ngelzarma, ya kuma bukaci hukumar sharia na kasa ta kafa kwamitin bincike dan gano ainhin masu laifi dan hukunta su.

KU KARANTA : 'Yan Najeriya guda 560 da suka dawo daga kasar Libya sun isa filin jirgin saman Fatakol

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarraya ta samar da ma’aikatan kula da harkokin makiyaya a fadin kasar dan cigaban su.

Alhaji Baba Ngelzarma, yace kungiyar MACBAN tayi maraba da matakan da gwamnatin tarayya ta dauka wajen ganin cewa an kawo karshen rikicin makiyaya da manoma a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng