Fusatattun matasa sun kaiwa soja farmaki saboda ya nemi soyayyar matar aure

Fusatattun matasa sun kaiwa soja farmaki saboda ya nemi soyayyar matar aure

- Fusatattun matasa sun kaiwa wani soja hari saboda yana neman soyayyar matar aure

- Sojan ya tsallake rijiya da baya

- Mijin matar ya tattara matasa domin su ja kunnen sojan

Wasu fusatattun matasa sun kaiwa wani soja farmaki bisa zarginsa da neman soyayyar wata matar aure a unguwar Gadumo dake Lokoja, Jihar Kogi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewar lamarin ya faru ne daf da wani gidan man fetur dake unguwar ta Gadumo ranar Talata da yamma.

Fusatattun matasa sun kaiwa soja farmaki saboda ya nemi soyayyar matar aure
Sojojin Najeriya
Asali: Depositphotos

Wani shaidar gani da ido dake kasuwanci kusa da wurin da abin ya faru ya ce sojan, da bai dade da zuwa garin ba daga Legas, yana ta kaiwa matar auren farmaki amma tana zukewa tare da bayyana masa cewar tana da aure.

Shaidar ya kara da cewa sojan bai daina kula matar ba duk da ta fada masa ita matar aure ce. Hakan ya saka mijin matar ya tunkari sojan har suka yi cacar baki.

DUBA WANNAN: Labari da duminsa: Rundunar sojin Najeriya ta hallaka yan ta'addan Boko Haram 57 yayin kazamin musayar wuta

Majiyar jaridar Daily Trust ta shaida mata cewar wasu fusatattun matasa a unguwar sun shigarwa mijin matar domin taya shi fada da sojan.

Shaidar ya ce sojan ya sha duka a hannun matasan kafin daga bisani wasu abokan aikin sojan su zo su kwace shi.

Da aka tuntubi kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Kogi, Mista Williams Aya, ya ce ba sanar da hukumar 'yan sanda faruwar lamarin ba.

Saidai ya ce jami'insu mai kula da ofishin unguwar da abin ya faru (DPO) ya tabbatarwa hukumar cewa ya fahimci an samu hargitsi a unguwar amma koda ya isa wurin sai aka fada masa cewar sojoji sun tafi da sojan. Kazalika ya ce jama'a sun ki bawa DPO din bayanin abinda ya faru.

Yanzu dai al'amura a yankin da abin ya faru sun koma dai-dai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng