Jama’an gari sun shiga taƙaddama a iyalan marigayi Chanchangi kan wani makeken Fili
An fara sakun taka tsakanin al’umman unguwar Kinkinau da Iyalan marigayi Alhaji Ahmadu Chanchangi kan wani katafaren fili da ya baiwa unguwar kyauta shekaru 14 da suka wuce, a cewar matasan unguwar.
Daily Trust ta ruwaito kimanin matasa 50 ne suka fita wata zanga zangar lumana a ranar Alhamis 11 ga watan Janairu, inda suke korafi kan batun da iyalan marigayin ke kokarin kwace musu Filin, wanda a yanzu haka an gine, inda aka gina karamin Asibiti.
KU KARANTA: Yaron Atiku yayi watsi da hukuncin Kotu, ya ƙwace Ɗansa daga hannun Uwarsa
Matasan sun bayyana ma majiyar Legit.ng cewa wasu daga cikin yayan Chanchangi sun dira asibitin tare da lauyansu dauke da siminti da babbar kofa, inda suka fasa katangar daya zagaye asibitin, da nufin rarraba filin a tsakaninsu.
Sai dai a yanzu haka Asibitin na samun gyara daga gwamnatin jihar Kaduna a wani yunkuri na inganta shi, tare da kara masa matsayi don amfanin al’ummar yankin Kinkinau dake karamar hukumar Kaduna ta kudu
Shugaban kungiyar al’mmar Kinkinau, Auwal Abubakar yace: “Mun ga dacewar mu janyo hankalin gwamnati da ma sauran jama’a ne bisa yunkurin da iyalan Chanchangi suke yi na raba asibitin gida biyu, don su siyar da sauran filin da ya ragu, wanda asibitin ke amfani da shi. “Mun yi zaton yayan marigayi zasu gaje shi wajen halin dattaku, amma sai ga shi abin kunya suna yi akasin haka.”
Shima Sarkin Kinkinau Alhaji Hudu Mohammed yace tun a shekarar 2003 Chanchangi ya basu kyautar filayen da suka kai Fuloti 20, don haka yake nuna bacin ransa da yunkurin yayan nasa na kwace abinda yake yi ma al’umma amfani.
Da aka tunkari daya daga cikin yaran mamacin, Usman Chanchangi, sai yace “Bani da ta cewa, maganan na gaban Kotu, don haka ku tafi Kotu.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng