Hukumar raya birnin Abuja za ta rushe wasu gine-gine 750
- Hukumar raya birnin Abuja ta ce za ta rushe wasu gine-gine 750 a yankin Lugbe
- Hukumar ta ce ba'a yi gine-ginen bisa ka'ida ba
- Darekta a hukumar, Mista Mukhtar Usman Galadima, ya sanar da hakan
Hukumar raya birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ce za ta rushe a kalla wasu gine-gine kimanin 750 a unguwar Lugbe domin kiyaye mazauna wurin fadawa cikin hatsari.
Darekta a hukumar, Mista Mukhtar Usman Galadima, ya sanar da haka yayin ziyarar yankin gine-ginen da abin zai shafa, yana mai bayyana cewar dukkan gine-ginen basu samu sahalewar hukumar ba kafin a gina su.
DUBA WANNAN: Gwamnati ta shirya yin karin kudin tikitin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
Galadima ya bayyana cewar anyi gine-ginen ne a karkashin babban layin wutar lantarki, kuma za'a rushe su domin bawa kamfanin raba hasken wutar lantarki sararin yin aiki da kuma kiyaye afkuwar hatsari.
"Nisan da hukuma ta yarda da shi tsakanin kowanne irin gini da babban layin wutar lantarki shine mita 30," a cewar Galadima.
Gine-gine dake Unguwannin Tudunwada da Peace Village ne rusau din zai fi shafa.
Ko a kwanakin baya saida ministan aiyuka, gidaje, da lantarki, Babatunde Raji Fashola, ya ce gwamnatin tarayya za ta rushe duk wasu gine-gine da aka yi a karkashin babban layin wutar lantarki da kuma wadanda aka yi ba bisa ka'ida ba a gefen hanyoyin gwamnatin tarayya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng