Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: Rundunar sojin Najeriya ta rasa wani jaruminta a ci gaba yaki da Boko Haram
Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana rasuwar wani jami’inta, Kyaftin M.M Hassan, a ci gaba da yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a wani shirinta na 'Operation Deep Punch'
Rundunar Sojoji ta kasa ta ruwaito cewa ta rasa wani mayakan soji, Kyaftin M.M Hassan, a ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda Boko Haram a wani shirinta na 'Operation Deep Punch'.
Kyaftin Hassan yana daga cikin rukuni na ‘Artillery Corps’ wadanda suke zaune a Damboa. Wannan jarumin soja dai an yaba shi cewa mutumi ne mai horo, kuma jami'in da ya fi dacewa, sakamakon haka ya sa abokan aiki da kuma yawan jama’a a wannan yankin suka sa masa suna - Sarkin Yakin Damboa.
Idan baku manta ba Legit.ng ta ruwaito cewa babban hafsan sojojin Najeriya, Laftana-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce kwanakin ‘yan ta’addan Boko Haram sun zo karshe a duniya don kuwa kwanan nan sojojin kasar za su murkushe su har abada.
KU KARANTA: Za mu ga karshen ‘Yan Boko Haram duk da ‘yan hararen da su ke kai wa – Buratai
A wani rahoto kimani 1,050 mayakan Boko Haram suka miƙa wuya ga dakarun soji a gabar tafkin Chadi da Monguno.
Fatanmu Allah yaji kansa da rahama, ya kuma kyautata namu karshe.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng