Yadda cutar 'Hepatitis' ke hana daukan matasan Arewa aikin soja
Ministan tsaro na Najeriya Alhaji Mansur Dan Ali, ya bayyana cewa cutar hepatitis wato ciwon kumburin hanta ita ke dakile cancantar mafi akasarin matasan Arewa daukar su aikin soja.
A cewar sa, mafi akasarin matasan Arewa da kokarin neman shiga aikin sojin kasa suna dauke ne da cutar hepatitis, wanda hakan yake assasa rashin nasararsu wajen cin ma burikansu.
Da wannan ne ministan yake janyo hankali iyaye akan su fara tura 'ya'yansu asibitin domin yi musu gwajin cutar kafin su nemi aikin soji.
Ministan ya bayyana hakan ne a yayin da ya halarci shirin tambayoyi da amsoshi mai taken Hannu da Yawa" da gidan rediyon Kaduna ke daukar nauyi, inda yace ana iya magance cutar.
Dan Ali ya kara jaddada kiranshi ga iyayen yara akan su dauki mataki na neman magance cutar wadda tana da magani a matakinta na farko kafin abin yayi kamari.
KARANTA KUMA: Al'umma sun yi ta Zomo: Tsageru sun yanke kan wani ma'aikacin tsaro a jihar Bayelsa
Yake cewa, duk da cewar cutar tana da magani amma hukumar dakarun soji ba zata bayar da aiki ga duk wanda yake dauke da cutar ba, ya kuma ce a halin yanzu akwai cutar hawan jini dake neman zama ruwan dare a cikin matasa.
Ministan ya kara da cewa, ya aika da sako zuwa ga ministan lafiya dangane da yadda cutar ke kara yaduwa a cikin al'ummar Najeriya domin a farga wajen daukar matakai cikin hanzari.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng