Tsohon mai baiwa gwamnan Taraba shawara ya musulunta

Tsohon mai baiwa gwamnan Taraba shawara ya musulunta

Tsohon mai baiwa gwamnan Taraba shawara kan harkokin siyasa, Mista Adamu Kwanci ya karbi musulunci.

Mista Kwanci ya ce bai yanke shawarar shiga addinin Musulunci ba sai da ya gudanar da bincike da dogon nazari, sannan karshen lamari ya gane cewar Musulunci shine Addinin gaskiya, sannan Musulmi sune jama'ar da su ka fi kowa son zama lafiya da tausayi.

Tsohon mai baiwa gwamnan Taraba shawara ya musulunta
Tsohon mai baiwa gwamnan Taraba shawara ya musulunta

Legit.ng ta samu cewa Mista Adamu Kwanci wanda a yanzu ya sauya suna zuwa Malam Adamu Muhammad Kwanci ya karbi kalmar shahada ne daga wajen Babban Malamin Addinin Musulunci nan mazaunin garin Jalingo Dakta Ibrahim Jalo Jalingo.

Sannan ya yi alkawarin zama jakadan Musulmi wajen wayar wa Kiristocin Jihar Taraba kai akan gaskiyar Musulunci da Musulmi, su gane karya da sharri da ake yi wa Musulmi a jihar da Nijeriya dama duniya baki daya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng