Ba mu sa a kamo shugaban kamfanin BUA ba – Rundunar ‘yan sanda
Rundunar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa bata da masaniya akan batun da aka dangana da rundunar na cewa ta sanya a kamo shugaban kamfanin BUA, Yusuf Binji.
A cewar kakakin rundunar na kasa Moshood Jimoh rundunar bata furta wani abu makamancin haka ba.
Ya kara da cewa basu ma san an kai wa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki hari bad a yaje filin aiki na BUA.
Ya kara da cewa idan har ma an kai wa gwamnan Edo hari, rundunar ‘yan sanda za su gudanar da bincike akai.
Idan ba a manta ba ana ta kai ruwa rana tsakanin kamfanin Dangote, da Bua kan wane ne mai asalin mallakin filin hako sinadarin hada siminti dake jihar.
KU KARANTA KUMA: Hukumar DPR ta rufe gidajen mai 4 a Ondo, ta yi gwanjon mai ga masu motoci
Gwamnatin Edo sun ce Yusuf Binji ne ya shirya wasu matasa su kai wa gwamnan hari da ya kai ziyara filin hako duwatsun.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng