Assha! Wanda ya lakadawa uban sa duka ya samu belin Naira 100,000
Mutumin nan katon banza mai suna Innocent Pitman da ake zargi da lakadawa uban sa duka sakamakon sabanin da suka samu ya samu beli a kotu mai matsayi na daya a unguwar Karu, garin Abuja babban birnin tarayya.
Mun samu dai daga majiyar mu cewa mutumin ya samu belin Naira Dubu dari kacal bayan da ya musanta zargin da ake yi masa a gaban alkalin.
KU KARANTA: Kyawawan hotunan wata mata da wadan mijin ta
Legit.ng haka zalika ta samu cewa a daren Alhamis 28/12/2017 wasu mahara suka kaddamar da kisan gilla ga dan kasuwa Alhaji Sule Itas/Gadau da ake yi wa lakabi da Lauya.
Kafin rasuwar sa shine Manajan kamfanin Gerawa Global Construction Company Limited, babban kamfanin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bude yayin ziyarar jihar Kano. Maharan sun kashe shi ne a gidan sa dake unguwar Tokarawa a jihar Kano.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng