Takaitaccen tarihin tsohon Gwamnan jihar Kaduna Marigayi Alhaji Lawal Kaita

Takaitaccen tarihin tsohon Gwamnan jihar Kaduna Marigayi Alhaji Lawal Kaita

Marigayi Lawal Kaita an haife shi ne a ranar 4 ga watan Oktobar shekara ta 1932 wanda kawo yanzu ya rasu ne yana da shekaru 85 a duniya.

Marigayi Lawal Kaita dai an haife shi ne a cikin garin Katsina a cikin tsatson iyalan Sullubawa dake sarautar Katsina din sannan kuma suna da dangantaka da marigayi tsohon Gwamnan jihar Katsina Alhaji Ummaru Musa 'Yar'aduna.

Takaitaccen tarihin tsohon Gwamnan jihar Kaduna Marigayi Alhaji Lawal Kaita
Takaitaccen tarihin tsohon Gwamnan jihar Kaduna Marigayi Alhaji Lawal Kaita

Alhaji Lawal Kaita ya yi karatun Firamaren sa a Katsina sannan ya halarci kwalejin Barewa dake garin Zaria a shekara ta 1946 zuwa 1950 kafin daga bisani ya halarci makarantar koyon tsimi da tanadi ta garin Landan a shekara ta 1971 zuwa 1972.

Marigayin ya yi aikin gwamnati a jihar Kaduna a ma'aikatar ruwa kafin faga bisani ya zama kwamishinan tsare-tsare da kuma mataimakin Sakataren din-din-din duk dai a jihar ta Kaduna.

Marigayin haka zalika yayi aiki a matsayin mai taimakawa shugaban kasa Shehu Shagari da kuma Cif Olushegun Obasanjo.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng