Ana shan bakar wahala a Najeriya – Inji Makarfi
- Tsohon shugaban PDP ya ce al’ummar Najeriya na shan bakar wahala a halin yanzu
- Makarfi ya ce idan aka yi la’akari da alkawuran da gwamnatin APC ta yi a baya da kuma irin rawar da ta taka zuwa yanzu, ba abin alfahari bane
- Tsohon shugaban ya bayyana cewa nan gaba darurruwa ‘yan siyasa zasu dawo PDP domin sun fahimci gwamnatin APC yaudara ce kawai
Tsohon shugaban jam’iyyar adawa ta PDP, sanata Ahmed Makarfi a lokacin da yake hira da jaridar Vanguard ya bayyana cewa al’ummar Najeriya na cikin mawuyacin hali.
Ya ce idan aka yi la’akari da alkawuran da gwamnatin APC ta yi wa jama’ar kasar kafin su karbi mulki da kuma irin rawar da suka taka zuwa yanzu, ba abin alfahari bane.
Ya ce: “Ana bakar wahala a kasar, harkokin tsaro na dada barbarewa, kuma sace-sacen mutane na karuwa da sauran su. Hakika za ku iya cewa ba laifin wannan gwamnati bane, amma zuwa yanzu ya kamata a ce gwamnati ta warware wasu matsalolin”.
Da aka yi masa tambaya yaya yake ganin zaben 2019 za ta kasance, Makarfi ya ce duk da dabarun jam’iyyar mai mulki, don janyewar babban jam’iyyar adawa hankali, nan gaba za a ga yadda darurruwa ‘yan siyasa zasu dawo PDP domin sun fahimci cewa wannan gwamnati yaudara ce kawai.
KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta yi wa 'yan Najeriya albishir kan lantarki da sufuri
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Makarfi ya bayyana cewa a jihar Kaduna, daya daga cikin jigo a siyasar jihar, Yaro Makama, ya canza sheka zuwa PDP a kwanan nan, kuma wannan na nufin ci gaba ne ga babban jam’iyyar adawa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng