Nada matattau a Gwamnati: Kataborar Buhari ya nuna Gwamnatin APC ba ta da fasali Inji PDP
- Gwamnatin Tarayya ta fitar da sababban nade-nade
- Sai dai a cikin jerin an samu sunaye matattau akalla 6
- PDP tace hakan ya nuna APC ba ta san inda ta dosa ba
Jama’iyyar adawa a Najeriya ta PDP tayi kaca-kaca da Gwamnatin APC bayan kwamacalar da aka yi wajen sababbin nade-naden ta na ma’aikatu da dama na Gwamnatin Tarayya a karshen wannan makon.
Babban Jam’iyyar adawa PDP ta soki nadin da Shugaban Kasar ya fitar kwanan nan inda a ciki aka samu sunayen matattu. Jam’iyyar tace wannan abin kunya ne wanda ya tabbatar da cewa APC ba ta san abin da ta ke yi ba kuma ba ta da tsari.
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta gina lantarki da hanyoyi
Sakataren yada labarai na Jam’iyyar Kola Ologbondiyan ne yayi wannan jawabi inda yace wannan katabora ya nuna dalilin da ya sa tattalin arzikin Najeriya yake cikin wani hali. An dai samu kura-kurai iri-iri a nadin da Gwamnatin tayi.
PDP ta soki Jam’iyyar mai mulki tace ta gaza shawo kan sha’anin kasafin kudi da sauran sha’anin ma’aikatan Gwamnti inda tace zai yi wahala a haka Jam’iyyar ta APC ta jagoranci Najeriya tayi gaba a sahun kasashen Duniya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng