Danlami Kurfi yayi kira ga gwamnati da ta karfafa maaikatar Asusun Daidatuwar Man Fetur na kasa wato PEF

Danlami Kurfi yayi kira ga gwamnati da ta karfafa maaikatar Asusun Daidatuwar Man Fetur na kasa wato PEF

Danlami Muhammad Kurfi shi ne mataimakin shugababan kamitin man fetur a majalisar tarayyar kasarnan a fannoni daban daban. Kwararrene kuma ya shahara a Harkar kasuwancin man fetur da gas sama da shekaru ashirin.

Kurfi ya ja hankalin gwamnati game da bunkasa aikin Asusun Daidaituwan Man fetur PEF (Maaikatar).

Yayi tsokaci kan magance mawuyacin layin da al'umma kasar nan ke fama dashi waken samun man fetur.

Yace: "Da farko dai, dole ne mu yarda da cewa ci gaba da kasancewa a cikin wannan mawuyacin wahalar man fetur ya zama tushen damuwa ga dukan al'ummar Najeriya saboda yawancin mutane na yau da kullum suna yin gwagwarmaya don samun man fetur da ba'a zaton haka ba. Amma, hakika, duk masu ruwa da tsaki zasuyi aiki don tabbatar da jituwa tsakanin masana'antu a wannan yanki kuma wannan shine dalilin da ya sa dole ne mu yaba wa duk wadanda suka yi nasara a kan dakile shirin PENGASSAN na zuwan yayin aiki.

Don magance wannan, gwamnati dole ne a kowane lokaci, ta tabbatar ta samar isasshen man fetur da rarraba shi a fadin kasar. Tabbatar da haka, dole ne 'yan kasuwar man su yi la'akari da bukatun 'yan Nijeriya fiye ribar da sue hange da kuma tallafawa kokarin gwamnati ta hanyar nuna jin kai a cikin kasuwancin su.

"Maganin warware matsalar wahalar man fetur zai yiwu kuma muma muna da rawar daza mu taka.

"Kwanan nan, kwamiti man fetur na Majalisar Dattijai ya yi kira da a rushewar hukumar da ke kula da Asusun Daidatuwar Man fetur PEF domin rashin aikin.

Kuna tsammanin irin wannan kira yana da kyau a lokaci kamar haka?

"Yawanci, ba na so in shiga al'amurar wasu abokan aikin da ke majalisar dattijai, bari in furta cewa irin wannan kira ba daidai ba ne.

"Da farko, muna bukatar mu san matsayin wannan hukumar hukumar ta PEF, to, a matsayinmu na rawa a cikin masana'antur man fetur, har sai munyi laakari da haka, duk kira don rushe hukumar , a ganina, ba shi da tushe. Rabuwar farashin man fetur abune da ka haifar da matsala a masana'antur man fetur.

"Kafin zuwan hukumar PEF matsalar ita ce 'yan kasuwar man fetur na la'akari da kudin sufuri ne domin fidda farashin da zasu sai da kayan. Don magance wannan ne, gwamnati ta kafa hukumar ta, PEF.

"Kamar yadda muka sani, an kafa asusun ne domin farashin man fetur ya kasance daidai a duk fadin Nijeriya. Kafin asusun ya farashin aiki, wannan sananne ne da cewa kasar nan, muna fuskantar raguwa a cikin samar da man fetur, rashin damar rarrabawa da kuma manyan nau'ikan farashi a sassa daban-daban na kasar. An yi amfani da shi don samar da asusun kuɗin da ake amfani da ita na kayayyakin man fetur kuma hakan zai bunkasa ci gaban tattalin arziki.

"Domin asusun yana yin aikin da ake tsammani, zamu iya magana akan daidaituwar farashin kayan a fadin kasar. Kuyi tsammanin a wasu lokuta da wasu 'yan kasuwan ba su daidata farashin famfo, sau da yawa, sun hadu da fushi na DPR, muna da farashi daya a fadin kasar. Hukumar ta PEF tana taka muhimmiyar rawa a wannan bangare cewa mafi kyaun da muke da shi a matsayinmu na masu ruwa da tsaki na iya yin shawarwari shi ne cewa ya kamata a ƙarfafa hukumar ta hanyar da zai sa ya kara inganta Najeriya da al'ummar ta.

"Kada ka manta cewa PEF ita ce hukuma kawai wadda ke riƙe da cikakkun bayanai na dukan kayan man fetur a fadin kasar nan. Ka yi la'akari da abin da halin zai kasance ba tare da asusun ba! Rugujeshi zai haifar da matsala ga 'yan Nijeriya a kowane bangare. Bari in gaya maku yanzu, idan muka rushe PEF kuma muyi amfani da ka'idoji na gida, to, 'yan kasuwar base da zabi illa su kara farashin kayan bisa la'akari da kudin sufuri kayan. Dukanmu mun san cewa kawo karshen hukumar kamar yadda wasu ke nunawa zai sa farashin kayan ya rarraba a fadin kasar nan, yayin da 'yan kasuwar za su sa farashin sufuri a farashin kayan.

KU KARANTA KUMA: Duk da karairayinku, yan Najeriya sun fi son Buhari – Shittu ga PDP

"Sakamakon haka, kudin sufuri na mutane da kayayyaki zai karu da haifar da damuwa kuma hakan zai samun a mummunar yanayin da dan Najeriya ke ciki. Don haka, ba tare da yin magana ba, ina tawali'u, kuma ina tsammanin abin da ake yi a cikin dukan muhimmancin gaskene ne, ya kamata mu yi aiki da hanyoyin zamani don kara ƙarfafa Hukumar don su yi aikinsu a mafi inganci.

"Za'a iya yin haka ne! Ta hanyar samar da dukkan kayan aikin da ake buƙata don inganta aikin yayi tasiri. Ɗaya daga cikinsu ita ce ta tabbatar da cewa hukumar ta samar da kudaden kuɗin da ya dace domin su iya biyan masu safari kuɗaden su a lokacin da ya dace."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng