Jos: Musulmi da Kiristoci na siyasa tare

Jos: Musulmi da Kiristoci na siyasa tare

- Matasan Musulmi da na Krista sun kafa kungiyoyin siyasa domin cudanya da juna

- Matasan sunce maimakon a rika amfani da su wajen bangar siyasa suma sun shiga siyasa

- Kungiyoyin suna taimakawa matasa yan uwan su wajen samar mu su aikin yi

Matasan Musulmi da na Krista suna cigaba da kafa kungiyoyin siyasa don cudanya da juna gabanin zaben kananan hukumomi da za a gudanar a watan Febrairu na shekarar dake zuwa.

Daraektan kungiyar Mista Lemark Peter yace sun kafa kungiyar matasa da ake kira YES 2019 dan hada kawunan matasan Musulmi da Krista, kuma cudanya da juna.

Mista Lemark Peter yace akwai kungiyoyi da dama ire-iren na su da suka shiga haraka siyasa, maimakon a rika amfani da wasu wajen bangar siyasa, suma sun shiga siyasar.

Shekarun baya matasa dake goyon bayan jam’iyyun sun salwantar da rayukan juna su amma yanzu sun gane yan siyasa amfani da su kawai suke yi.

KU KARANTA : El-Rufai da Lai Mohammed shahararrun maƙaryata ne - Jam'iyyar PDP

Dalili da ya sa suka kafa kungiyoyin da za su rika taimakawa junan su maimakon bangar siyasa.

Bala Buswat wani matashi daga karamar hukumar Kanam ya ce suna samar wa yan uwansu matasa sana'o'i ta hanyar kungiyoyi da suke kafa.

Jos: Musulmi da Kiristoci na siyasa a tare
Jos: Musulmi da Kiristoci na siyasa a tare

Yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaben 2019, shugabanin matasan jihar Filato sun ce za su isar da wannan kyakyawar manufa ta su ga sauran yan uwansu matasa da ke wasu jihohi, musamman jihohin da a kan fuskantar tashe-tashen hankula na addini a cewar Mr Polycarp Job mataimakin daraktan kungiyar siyasa ta Yes 2019 a jihar Filato.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng