Matsalar shigar banza a tsakanin Maza da Mata a jami’o’in Arewa, laifin wanene?

Matsalar shigar banza a tsakanin Maza da Mata a jami’o’in Arewa, laifin wanene?

A yanzu kam a iya cewa matsalar shigar banza bata tsaya a kan mata kadai ba, tun da maza ma sun tsunduma cikin mummunan al’adar duk da cewa makarantun gaba da sakandari na sanya tsatstsauran dokoki don hana abin, amma ya ci tura.

Wakilin jaridar Daily Trust Umar ya zanta da wata dalibar jami’ar Bayero, Halima dake Kano ta koka kan yadda wasu matan suke shigar banza tare da nuna tsiraici: “Wasu matan na ganin ba su cika ba, har sai sun rike manyan wayoyi, ta kashe kudi kamar kamar ba gobe, da mallaki mota, sa’annan ta mallaki mota.”

KU KARANTA: Rashin aikin yi: Har da masu digirori a neman aikin koyar da ýan Firamari a jihar Kaduna

Ita ma, wata daliba mai suna Rahama Ibrahim ta ce yawancin yan mata na kwaikwayon shigar banza ne daga kawayensu, don haka a ganinta kawaye na tasiri a kan kawayensu. Yayin da daliba Rabi Malah Bukar ta bayyana shigar banza da mata ke yi a matsayin wani hanyar jan hankulan maza.

Matsalar shigar banza a tsakanin Maza da Mata a jami’o’in Arewa, laifin wanene?
laifin wanene?

“Da yawa daga cikin mata basu da godiyar Allah, kuma basu da wadatan zuci, don haka sai su fara shigar banza don maza su dinga kula su, suna basu kudi, wasu kuma saboda basa mayar da hankali a karatu, sai su fara bin Malamansu da nufin su dinga basu maki kyauta.”Inji Rabi.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban tsangayar sashin sadarwa na jami’ar Bayero Farfesa Umar Pate ya daura laifin shigar banza da dalibai ke yi a kan iyayensu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng