Ban san yadda ake neman kudi ba - Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce bai iya neman kudi ba
- Buhari ya ce sai da yaci bashin banki kafin ya gina gidan sa na Abuja, Kaduna da na Kano
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace babban matsalar sa a rayuwa shine bai iya neman kudi ba.
Buhari yace sai da yaci bashin banki kafin ya gina gidan sa na Daura, Abuja, da na Kaduna.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya zanta da majiyan jaridar SUN.
Gwamnatin Murtala da Obasanjo, sun tabbatar da duka manyan ma’aikata da sojoji sun bayyana kadarori da suka mallaka a lokacin da za su fara aiki da lokacin da za su yi ritaya.
KU KARANTA : Da hanun karfe za ka yaki cin hanci da rashawa a Najeriya – Tsav ya shawarci Buhari
“Hadda shanu na sai da na bayyana adadin su, duk da yiwuwar za su rika haihuwa a kowani shekara
Saboda haka idan mutane dagasake suke, suna son su san ainihin ma’aikatan gwamnatin da suka yi arziki, su yi bincike daga zamanin Murtala zuwa kasa. lokacin za su tausaya wa ire-iren mu da basu iya neman kudi ba.
“Kowa yana son kudi, amma ban iya neman kudi ba. Idan kuka yi bincike za ku ga yadda na ci bashin banki kafin na gina gida na, na Daura, Abuja da na Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng