Tuna baya: Halin da muka tarar da gawar Janar Sani Abacha bayan mutuwarsa - Gidado Idris

Tuna baya: Halin da muka tarar da gawar Janar Sani Abacha bayan mutuwarsa - Gidado Idris

Tsohon sakataren gwamnati na zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha, Alhaji Gidado Idris wand ya rasu a ranar Juma’ar data gabata 15 ga watan Disambar 2017 ya bayya halin da suka tsinci gawar Abacha a ranar da ya rasu.

Cikin wani hira da yayi da jaridar Daily Trust, Gidado ya bayyana cewa a da misalin karfe 8 na safiyar ranar Litinin 8 ga watan Yunin shekarar 1998 aka kira shi a waya, babban sufetan Yansanda na kasa, Coomassie ne ya kira shi, inda ya nemi shi ya taho Villa da hanzari.

KU KARANTA: Inna Lillahi wa inna Ilaihi raji’un: Allah ya yi ma Sule Katagum, Wazirin Katagum 95, rasuwa

Sai dai Gidado yace yana daya daga cikin na hannun daman Abacha, wanda tun Abacha na mukamin Manjo suke tare a Kaduna, inda suke zuwa wasan kwallon Tennis, wata rana ya taba fada ma Abacha cikin raha, “Abacha, ina ganin wata rana zaka iya shirya juyin mulki, kuma ka mulki Najeriya, idan ka zama, kada ka manta da ni.”

Tuna baya: Halin da muka tarar da gawar Janar Sani Abacha bayan mutuwarsa - Gidado Idris
Abacha da Useni

Aikuwa haka aka yi, a ranar 17 ga watan Oktoban 1995 Abacha ya nada shi sakataren gwamnatinsa, har zuwa 1999, don haka aminan juna ne, inda Idris yace a kowanne karshen mako sai ya je Villa sun gaisa da Abacha, kuma a sha hira, kamar yadda ya shaida ma majiyar Legit.ng.

“Na isa Villa da misalin karfe 8:30 bayan na karya, da isa ta sai an zarce ofishin na, inda na tarar da Abdulsalami Abubakar, bayan nan sai sauran manyan jami’an gwamnati suka iso, babban hafsan Sojan kasa, Ishaya Bamaiyi ne ya umarce ni na je na duba ko Abacha zai haralci taron.

“Shiga ta dakin da muka saba hira da Abcha ke da wuya sai na tarar da Maryam Abacha, Mohammed, Gwarzo da kuma Buba Marwa, a nan ne Gwarzo ya fada mana Abacha ya rasu.” Inji Idiris

Tuna baya: Halin da muka tarar da gawar Janar Sani Abacha bayan mutuwarsa - Gidado Idris
Gidado Idris

Sai dai ya kara da cewa a lokacin daya hau zuwa dakin Abacha don ganin gawarsa, sai ya tarar da gawar zaune a kan kujera, tare da maganin shaka na masu cutar Asthma (Inhaler) a kasa, wanda ya fadi daga hannunsa.

“Duk da cewa a ranar ALhamis kafin mutuwarsa mun tattauna, kuma na ji shi yana tari, amma ban taba sanin yana da Athma ba, kawai dai na yi tunani yana mura ne, amma ban san abin yayi tsanani ba. Don kai tsaye ba zan iya cewa kashe shi aka yi ba.” Inji shi.

Game da shugabancin Najeria kuwa, Gidado yace shi ne ya jagoranci zaman da aka zabi sabon shugaban kasa bayan mutuwar Abacha, inda yace bayan an binne gawar Abacha a Kano, sai suka koma Abuja don cigaba da tattaunawar da suka fara don zaben sabon shugaba.

“A zaman da muka yi, Jeremiah Useni ya bayyana muradinsa na zama shugaban kasa a matsayinsa na babban hafsan Soja bayan Abacha, amma sauran sun fi kaunar Abdulsalam ya zama, ko da yake duk mukaminsu daya, laftanar janar,

“Nan da nan kowa ya gamsu da Abubakar, sai shi da kansa Jeremiah Useni ya nemi a kara ma Abubakar girma zuwa mukamin Janar gaba daya, a nan take ya ta shi ya sara ma Abubakar, ni kuma sai na umarci Alkalin Alkalai Muhammad Uwais ya baiwa Abdulsami rantsuwa, ni kuma na kai shi Ofis, na gyara masa kujera ya zauna daram.” Inji marigayi Gidado Idris.

Allah ya jikansu gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng