Dandalin Kannywood: Jerin Fina-finai 5 da kar ka sake a baka labari
A sakamakon gabatowar karshen shekarar 2017, a yau dandalin na Kannywood ya kawo muku jerin fina-finai 5 da suka yi fice wajen shahara ta fuskar nishadantar wa da kuma debe kewa wanda bai kamata a ce sun wuce bamu ganewa idanun mu ba.
Legit.ng ta kawo muku jerin fina-finai biyar na Kannywood da suka zamto zakarun gwajin dafi a shekarar 2017 da ya zamto kusan wajibi akan mu da mu arasa musu lokutan mu.
1. Safara
Wannan fim din yayi fice wajen buga misalin da nazarin yadda batun cinikin dan Adam a Arewa maso gabashin Najeriya.
Jaruman wannan shiri sun hadar da; Aina’u Ade, Ali Nuhu, Abba El-Mustapha, Ladidi Fagge, Jamila Nagudu da kuma Isa Isa.
2. Mansoor
Wannan shirin yayi matukar shahara a shekarar nan ta 2017, inda batutuwan sa ke ci gaba da gudana a bakunan al'umma, wanda ya malalo yadda wasu daliban makaranta suka shaku da juna sai dai kash azzalumai da 'yan bakin ciki suka kafa musu kahon zuka.
Jaruman wannan shiri sun hadar da; Ali Nuhu, Maryam Yahya da kuma Babbale Hayatu.
3. Rariya
Wannan shirin na rariya da Yaseen Auwal ya jagoranta yayi nazari ne akan labarai na daliban makanta ta 'yan mata da ke nuna yadda rayuwar wadanda suka fito daga gidaje daban-daban ke kasancewa a makaranta.
Jaruman wannan shiri sun hadar da; Rahama Sadau, Ali Nuhu, Hafsat Idris, Maryam Booth, Fati Washa, Sadik Sani Sadik da makamantan su.
KARANTA KUMA: Rundunar 'yan sanda ta cafke wani babban kwamandan Boko Haram a jihar Borno
4. Auren Manga
Wannan shiri ya kunshi jarumai irin su Hadiza Gabon, Suleiman Yahaya da Falalu Dorayi, inda yayi nazari akan ban dariya da zai nishadantar da masoya fina-finan hausa.
5. Kalen Dangi
Wannan shiri ya kunshi soyayya, daukaka da daraja, karya tare da cin amana, inda jarumai irin su Ali Nuhu, Aminu Momo, Fati Washa da Sadiq Sani Sadiq suka nuna gogewar su da kwarewa.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng