Kasar Rasha ta girgiza Amurka da makamin kare dangi

Kasar Rasha ta girgiza Amurka da makamin kare dangi

Kasar Rasha ta girgiza 'yan hanji na cikin shugaban kasar Amurka, Donald Trump, sakamakon hannun ka mai sanda da sanadin ministan tsaro na kasar Rasha, Viktor Bondarev, wadda ta firgita Amurkawa.

Viktor wanda yayi nunin yatsa tare da gargadin Donald Trump, akan cewa in har kasar sa za ta juya baya ga yarjejeniya ta makamai da kasashen suka rattaba wa hannu, to tabbas kasar ta Rasha za ta ci gaba da kera makaman kare dangi wandanda za su yiwa na Amurka zarra ta kowace fuska.

Makamin kare dangi
Makamin kare dangi

A sakamakon wannan sanarwa ta kasar Rasha ne ya sanya al'ummar kasar Amurka suke zaman dar-dar da kuma tashin na fadar gwamnatin kasar dake birnin Washington DC, domin kawo wa yanzu kasar Amurka ba ta ce uffan ba don mayar da martani.

KARANTA KUMA: Bode George ya janye takarar sa ta shugabancin jam'iyyar PDP

Da yake jawabin na sa da manema labarai, ministan tsaro na kasar Rasha ya bayyana cewa, " Kasar Rasha a shirye take da tayi watsi da yarjejeniyar da suka kulla kuma ta sani cewa, kera makaman kare dangi cikin kankannin lokaci ba wani abu ne zai daga hankalin kasar ba."

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng